Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ce yana bin abokan huldarsa a jihohin Kano, Katsina da Jigawa bashin da ya kai Naira biliyan 17 da miliyan 589.
Basussukan, a cewar kamfanin sun taru ne tsakanin watannin Janairu da Disambar 2020.
- KEDCO ya fara raba mitocin wutar lantarki kyauta a Kano
- Hamar: Kabilar da mata ke shan duka kafin a aure su
A ciki wata sanarwa da shugaban Sashen Watsa Labarai na Kamfanin, Ibrahim Sani Shawai ya fitar, KEDCO ya ce kudaden sun taru ne sakamakon ko dai kin biyan kudin dungurungun, biyan wani kaso, ko kuma biyan rabin kudaden wutar da abokan huldar tasu suka sha.
Kamfanin ya ce matukar abokan huldar nasu suka biya basukan da ake binsu, za a sami ingantuwar samun wutar a jihohin.
“Harkar kasuwanci muke yi, kuma dole ne mu ma mu biya abokan huldarmu kudaden wutar da muka sayo daga wurinsu dari bisa dari ba tare da rage ko sisi ba,” inji shugaban kamfanin, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna.
Dagan an sai ya kara yin kira ga jama’a kan su daure su biya basussukan da ake bin su domin kamfanin shima ya samu ya biya wadanda yake sayo wutar daga wurinsu kuma a sami karin wadatuwarta.