Kotu ta yanke wa tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Hulda Jama’a, Doyin Okupe, hukuncin dauri a gidan yari kan lafin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta kama shi da laifuka 26, sannan ta yanke mishi hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari a kan kowanne laifi.
- An kama dan Najeriya da miyagun kwayoyi na N18m a Indiya
- Najeriya ta sami tiriliyan 1.3 ta hanyar noman rake a shekara 10
Ta kuma ci shi tarar Naira miliyan 13, tare da ba shi zabin biyan Naira dubu 500 a maimakon kowane hukuncin da ta yanke mishi na zama a gidan yari.
Sai dai ta ce idan ya gaza biyan tarar kafin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, za a tisa keyarsa zuwa gidan yari.
A 2019, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da Doyin Okupe a gaban kotu kan tuhume-tuhume 59 kan halasta kudaden haram da karkatar da Naira miliyan 240 daga hannun Kanar Sambo Dasuki, tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro.
EFCC ta gurfanar da tsohon hadimin shugaban kasan ne tare da wasu kamfanoni biyu: Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.
Alkalin kotun ta ce ta yanke hukuncin ne bayan sauraron koken neman sassauci da wasu manyan ’yan Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife da kuma Shugaban Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), Idi Farouk da matar Okupe, molara da kuma dansa.
A cewarta Okupe ya yi jayayyar karbar miliyoyin kudaden da ake zargin sa da karkatarwa.
Ta kara da cewa yi ta masa sassauci ne bayan gano cewa wannan ne karo na farko da ya taba bayyana a gaban kotu a matsayin wanda ake tuhuma.