Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar ficewa daga cikin wasu kungiyoyi na duniya kusan 90, sakamakon dawainiyar da ke tattare da hulda da kungiyoyin.
Majalisar Zartarwa ta kasa ce ta dauki wannan matakin a taronta na shekaranjiya Laraba da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagiranta.
Yanzu haka Najeriya wakiliya ce a cikin kungiyoyi duniya 310, wadanda kuma suke bin ta kudin karo-karo da ya kan Dala miliyan 120 (kimanin Naira biliyan 43) da ya kamata ta bayar a matsayin tata karo-karon na raya kungiyoyin.
Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta bayyana wannan mataki na rage kungiyoyin da Najeriya za ta kasance a ciki da kusan rubu’i lokacin da take bayani ga manema labarai na Fadar Shugaban kasa bayan kammala zaman majalisar.
Ta ce, gazawar Najeriya ta biya kudin karo-karon yana jawo mata wulakanci, inda wasu kungiyoyin duniya suka fara korar Najeriya daga tarurrukansu saboda bashin da suke bin ta.
Ministar ta ce, a duk shekara Najeriya tana biyan kudin karo-karo Dala miliyan 70 bayan ga wanda ake bin ta bashi a baya. Adeosun wadda ba ta bayyana kungiyoyin da Najeriya za ta fice daga cikinsu ba, ta ce shugabannin kasar nan na baya sun yi ta yin alkawuran da ba a tanadi kudinsu ba.
Ta ce Majalisar Zartarwa ta umarci a daddale bashin da ake bin kasar nan tare da tsara yadda za a biya domin kauce wa jin kunya a idon duniya.
Ministar ta ce majalisar ta bayar da umarnin a fitar da takardar sanarwar gwamnati da za ta kayyade wadanda za su rika daukar alkawari a madadin Najeriya domin “An gano darakta ko jakadan da ya halarci taro kan yi alkawari a madadin Najeriya. Kuma daga nan kungiyoyin na duniya sai su rika farautar kudinsu daga gare mu,” inji ta.
Shi ma Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, akwai kungiyoyi birjik na duniya da Majalisar dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da Najeriya ta shiga cikinsu wadanda kuma dukansu akwai bukatar gudummawar da duk kasar da ke cikinsu sai ta bayar a karshen kowace shekara.
Malam Garba Shehu, ya ce saboda irin wadannan kudaden gudummawar tafiyar da kungiyoyin da Najeriya ba ta biya ba, har ta kai idan aka je taro akan bukaci mai wakiltar Najeriya da ke wajen ya fita daga taron. Ya ce hakan ba karamin abin kunya ba ne ga Najeriya.
Don haka Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, ya kamata a sake lale, inda za a baje kungiyoyin a faifai a zabi wadanda suke da amfani ga kasar don a ci gaba da tafiya da su.
Ya ce wasu basussukan da ake bin Najeriya, tun na shekara da shekaru ne, don haka a kididdige su abu ne mai kamar wuya. Ya ce, ba matsi ne ya sa Najeriya za ta fice daga wadannan kungiyoyi ba, sanin ciwon kai ne kawai.