Ta wace hanya zan iya mallakar eNaira? Wannan sabon tsari yana dauke ne da manyan matakai guda biyu.
Matakin farko shi ne ya kunshi alaka ce a tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran bankunan kasuwanci (Commercial banks).
- Kudin e-Naira: Ma’ana, fa’idoji da tsarin gudanuwarsa (1)
- CBN ya fito da kai’idojin amfani da e-Naira
Mataki na biyu kuma tsakanin bankunan kasuwanci ne da masu ajiya.
A matakin farko, Bankin CBN zai bai wa bankunan kasuwanci damar isa ga tsarin, tare da bude musu asusun ajiyarsu ta Intanet (eNaira Wallet), wanda yake dauke da adadin abin da suka saya na e-Naira.
A karkashin wannan tsari ne zai ba su damar bude wa masu ajiya asusunsu su ma, da ba su damar iya saya musu nasu nau’in eNaira din, ta amfani da babbar magudanarsa (CBN Blockchain).
Sai mataki na biyu, wanda zai kasance a tsakanin bankunan kasuwanci da masu ajiya.
A wannan mataki, bankunan kasuwanci za su yi mu’amala ce da nau’in mutane biyu.
Na farko su ne masu taskar ajiya a bankunansu. Na biyun kuma wadanda ba su da taskar ajiya a kowane banki.
Idan kana da taskar ajiya a bankinka, da zarar an fara amfani da wannan tsari, bankinka zai aiko maka sako ta lambar wayarka, ko akwatin Imel dinka.
Sakon yana dauke ne da adireshin da za ka bi, don saukar da manhajar da za ka yi amfani da ita wajen bude taskar ajiya ta magudanar bankin CBN (CBN Blockchain), wato: eWallet ko Digital Wallet.
A wannan taska ce za ka rika karba da aika nau’in kudin e-Naira, kai-tsaye.
Da zarar ka bude taskar, kana iya loda kudi daga taskarka mai dauke da takardun kudi, zuwa taskarka mai dauke da eNaira, kai-tsaye, kuma a kyauta, babu wani caji.
Misali, idan kana da taskar ajiya a GTBank, ko Jaiz Bank, kuma kana son aika Naira 20,000 zuwa sabuwar taskarka ta eNaira, sai ka hau taskarka ta amfani da manhajar bankinka ko ta amfani da lambobin USSD ta wayar salula, ka aika kai-tsaye, babu wani jinkiri.
Da zarar ka aika, nan take kudaden za su shiga taskarka ta eNaira.
Daga nan kana iya amfani da wadannan kudade wajen aika wa wani mai taskar eNaira, ko ka sayi kayayyaki da su kai-tsaye a shagunan saye da sayarwa na Intanet (Internet online stores).
Idan kuma ba ka da taskar ajiya da wani banki, kana iya amfani da lambar wayarka mai rajistar NIN (lambar katin shaidar dan kasa-National Identity Number) wajen sayen eNaira kai-tsaye, idan adadin kudaden da kake bukata bai su shige Naira dubu 50 ba a yini.
Tsare-tsaren da za su sauwake faruwar hakan, tare da ka’idoji da kuma lambobin da za a yi amfani da su wajen yin hakan, duk za su zo a fayyace nan kusa.
Yaya karbuwar wannan kudi yake a duniya?
Ba ka da matsala wajen hakan. Yadda takardar kudin Najeriya take halattacciya kuma amintacciya wajen kasuwanci, haka wannan nau’in kudi na eNaira yake halattacce.
Da zarar ka loda wani adadi na kudi a taskar eNaira Wallet, za ka iya aiwatar da cinikayya da shi kai-tsaye, a kowane shagon sayar da kayayyaki. Koda kuwa farashin hajar na wata kasa ce daban. Wannan ba damuwa ba ce.
Da zarar ka shigar da bayanan taskar ajiyarka ta eNaira, nan take tsarin zai kimanta adadin kudin da za ka biya da eNaira, gwargwadon farashin kudin kasar da ka aiwatar da cinikayya da shi.
A daya bangaren kuma, kana iya aika wa dan uwanka ko wani naka wannan nau’in kudi a ko’ina yake a duniya, ta amfani da lambarsa ta eNaira Wallet idan yana da shi, ko ta taskar ajiyarsa a ko’ina yake a duniya.
Idan ina son ciro kudin a zahiri kuma fa?
Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka. Sai kawai ka loda kudin zuwa taskar ajiyarka na banki.
Daga nan ka yi amfani da katin ATM dinka ka ciro su. Ko ka je bankinka ka cira kai-tsaye. Ko kuma ka aika wa wani a taskarsa, shi kuma ya ba ka takardun kudi.
Wannan bai takaitu ga adadin kudin da wani ya aiko maka ta manhajar eNaira Wallet dinka ba kadai.
Hatta adadin kudin da ka loda daga taskar ajiyarka na banki, sai daga baya ka ji kana bukatar ka dawo da su don ka cire saboda wasu bukatu ko lalurar rayuwa da ta shafi kudi, kana iya sake dawo da su taskar ajiyarka ta banki kai-tsaye, ba tare da wani caji ba, sannan ka cire su don biyan bukatarka.
To, yaushe ne wannan sabon tsari zai fara aiki?
A karon farko, Babban Bankin Najeriya (CBN), ya yi niyyar kaddamar da sabon tsarin ne a ranar 1 ga watan Oktoba, daidai da lokacin da kasarmu take bikin murnar cika shekara 61 da samun ’yanci daga Turawan mulkin mallaka, amma ‘yan awanni kafin wayewar gari, sai ya canja lokaci.
Ana sa ran nan gaba kadan za a bayyana sabuwar ranar da za a kaddamar.
Wannan kaddamarwa don yin gwaji ne na tsawon wata uku, wanda zai tike a karshen wannan shekara.
Daga nan kuma sabon tsarin zai game kasar baki daya.