Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta girke dakaru na musamman domin yakar matsalar tsaro a Kudancin Jihar Kaduna.
Kwamandan Rundunar Sojin Sama da ke Kaduna, Air Vice Marshal Musa Mukhtar ya ce tura dakarun ya biyo bayan umarnin shugaban kasa na tabbatar da tsaro da zaman lumana a yankin.
“Dakarun za su ci gaba da zama a Kudancin Kaduna matukar akwai bukatar yin hakan, kuma mahukunta za su hada karfi da sauran hukumomin tsaro domin magance kashe-kashe da wanzuwar zaman lafiya”, inji shi.
Ya ce mayakan da suka hada da sojoji 28 da hafsoshi biyu da kuma likitoci za su kara wa takwarorinsu da Hedikwatar Tsaro ta tura yankin a kwanakin baya kaimi.
Don haka ya bukace su da su kiyaye hakkokin dan Adam da nuna kwarewa yayin gudanar da aikinsu.
Ya kara da cewa rundunar za ta rika kai wa dakarun taimako karkashin rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike.
– Matsalar tsaro a Kudancin Kaduna
Yawaitar tashe-tashen hankula a Kudancin Kaduna na yawan damun mutane a sassan Najeriya.
A kwanakin da suka gabata an yi ta taruka kan matsalar tsaro da ta ki ci, ta ki cinyewa a Arewacin Najeriya tsakanin Shugaba Buhari da shugabannin tsaron kasa.
A watan Yuli Majalisar Wakilai ta gabatar da kudurin neman bangaren zartaswa ya kawo karshen kashe-kashe a Kudancin Kaduna.
Rikice-rikice da suka hada da kai hare-hare da ramuwar gayya bisa dalilan kabilanci da sauransu sun yi ajalin mutane da yawa a yankin tare da tilasta wa wasu gudun hijira baya ga asarar dukiyoyi.
Wasu al’ummomi ba sa iya zuwa gonaki saboda tsoro a yankin, saboda ci gaban hare-haren duk da dokar hana fita ta sa’a 24 da gwamnatin jihar ta sanya na makonni.
A baya-bayan nan an kashe mutum 19 a wani hari da aka kai a kauyen Kukum Daji a Karamar Hukumar Kaura ta Jihar ta Kauda.