Matar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, Misis Aduke Obasanjo, ta ce bai kamata mata su zauna suna jiran mazajensu su ba su hakuri ba, matukar suna son zaman lafiya a zamantakewar aurensu.
Ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wani taro a hedkwatar majami’ar Celestial Church of Christ, da ke Ketu, a Jihar Legas ranar Lahadi.
- Majalisa ta nemi a yi wa matasan NYSC karin kudin abinci
- ’Yan bindiga sun cinna wa gonakin manoman da suka ki biyansu ‘haraji’ wuta a Neja
Rahotanni sun ce Misis Aduke, wacce ta wakilci mijin nata a wajen bikin, ta shawarci mata kan yadda za su rike aurensu ba tare da sun nemo wani ya yi musu sasanci ba.
Ta kuma shawarci mata, musamman wadanda suke daukar wani nauyi a gidansu da su guji amfani da damar wajen raina mazajen nasu.
A cewarta, “Matan da suke daukar nauyi a gidajensu, yana da kyau su fahimci cewa Allah ne ya ba su wannan damar. Bai kamata su yi amfani da ita ba wajen raina mazajensu.
“A maimakon su jira mazajensu su ba su hakuri, su ya kamata su ja su ta lallama har zuwa daki su sasanta a can.
“Duk abin da ki ka aikata ki sani zai yi tasiri a kan ’ya’yanki. Yadda kike mu’amalantar mijinki na da tasiri sosai,” inji ta.