Shugaban Buhari ya bukaci iyaye kada su goyi bayan ’ya’yansu a kan sata da lalata dukiyoyin jama’a da miyagu ke yi a sassan Najeriya.
Ya roki iyaye da matan aure da su kora ’ya’yansu ko mazajensu idan sun zo gida da kayan da ba su san daga inda suka samo su ba.
- ‘Gwamnati ba ta ce gwamnoni su jibge kayan tallafi a rumbuna’
- Matasa sun fasa rumbun abincin Adamawa
- Mutane sun saci taki da iri mai guba a matsayin abinci
- An sace magunguna masu hadari a ma’adanar NAFDAC
Shugaban Kasar ya yi kiran ne a sakonsa kan fara zaman Kwamitin Binciken Shari’a na Gwamnatin Jihar Legas kan koke-koken da zanga-zangar #EndSARS ta haifar da zai fara aiki ranar Litinin.
Ya bayyana cikakken goyon bayansa ga yin adalci ga jami’an tsaro da masu zanga-zangar lumanar da aka kashe da kuma mutanen da aka lalata dukiyoyinsu a tarzomar.
Ya jadadda mahimmancin zaman lafiya da hadin kai da kaunar juna tsakanin ’yan Najeriya sannan ya yi hani ga nuna kiyayya da kuma cin mutumcin juna.
Buhari ya ce jami’an tsaro za su tabbatar da dawowar tsaro a kasa kuma gwamnatinsa na aiki tukuru domin kyautata rayuwar al’umma musamman matasan da ba su da aikin yi.
Ya ce gwamanti na kuma kokarin saukaka rayuwa daga matsin da annobar COVID-19 ta haifar sannan ya yi gargadi a kan sace-sace da kuma lalata dukiyar jama’a.