Sugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gargadi hukumomin tsaron sirri da su guji abin da ka iya kawo tsaiko ga aikin hukumarsu gabanin babban zaben 2023.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, lokacin da yake kaddamar da sabbin rukunin gidajen hukumar tsaron sirri ta kasa a unguwar Karmo da ke Abuja.
Buhari ya kuma bukaci wadanda ke da alhakin gudanar da ayyukan zabe daban-daban, musamman rarrabawa da kuma lura da kayayyakin zaben, da su yi aiki da kwarewa.
Kazalika ya ce kokarin hukumar na samar da gidajen ma’aikatan ya yi daidai da burinsa na cimma ingantaccen tsaro a Najeriya.
Da yake jawabi, babban hafsan tsaron rundunar, Manjo Janar Samuel Adebayo ya ce an samar da rukunin gidajen ne domin magance kalubalen matsugunin da hukumar ke fuskanta.
Ya kuma yi alkawarin hukumar za ta aiwatar da umarnin shugaban kasan na samar da tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri yadda ya kamata.