✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku fara duba jinjirin watan Sha’aban —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi da su fara duban watan Sha’aban daga ranar Litinin.

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi da su fara duban watan Sha’aban daga ranar Litinin.

Sarkin Musulmi ya sanar da haka ne ranar Lahadi ta hannun Shugaban Kwamitin Shura na Harkokin Muslunci a Fadar Sarkin Musulumi, Farfesa Sambo Junaidu.

“Muna sanar da al’ummar Mususlmi cewa daga ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Rajab shekara ta 1444 Hijiriyya, za a fara neman jinjirin watan Sha’aban.

“Duk wanda Allah Ya sa ya dace da ganin watan, ya hanzarta sanar da dagaci ko mai unguwarsu, don ya snar da mu”, a cewar Sanarwar.

Daga nan ne kuma ya yi fatan Musulmi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na addini lafiya.