✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ku daina tsammanin komai daga Buhari – Obasanjo ga ’yan Najeriya

Ya ce iya kokarin Buhari kenan, ba zai iya yin wani abu sama da haka ba.

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce jiran tsammanin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wani abu sama da wanda yake yi daidai yake da jiran gawon shanu.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin wani taro kan hanyoyin bunkasa tsaro da wata kungiya mai suna Global Peace Foundation and Vision Africa ta shirya a Abuja.

Obasanjo ya ce, “Gaskiya daya ce, Buhari ya yi iya bakin kokarinsa, iyakar abin da zai iya yi kenan. Idan muka ce sai ya yi sama da haka, to tabbas yaudarar kanmu muke yi.

“Ina muka dosa kenan? Ba zai yiwu mu zauna mu nade hannuwanmu ba. Na yi amanna wannan na daga cikin abubuwan da muke yi. Yaya Najeriya za ta kasance bayan ya tafi? Addu’a ta ita ce Allah Ya ba shi tsawon rai ya kammala mulkin nan lafiya.

“Amma me ya kamata mu yi wajen inganta yanayin da muke ciki a yanzu? Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyanmu baki daya,” inji shi.

Tsohon Shugaban ya kuma ce amfani da karfin soja kadai ba zai kawo karshen matsalar ta’addanci ba a Najeriya, dole sai an hada da wasu dabarun.

Ya kuma ba da shawarar a kirkiri ’yan sandan jihohi, inda ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi yankuna, kuma kowane yanki shi ya fi sanin hanyoyin magance nasa.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, kira ya yi ga shugabanni da su daina siyasantar da harkokin siyasa.

“Jam’iyyu na zargin junansu da gazawa wajen magance matsalolin tsaro, ina ganin wannan ce babbar matsalar da muke fuskanta a Najeriya yanzu. Mun yi amanna akwai matsala, kuma mafita na nan kusa, babu abin da za a yi sai da zaman lafiya. Dole ne mu koma ga litattafan addinanmu don lalubo bakin zaren,” inji Sarkin.