✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku daina hulda da masu yi wa Kwastam sojan gona – Kwaturola

Hukumar Kwastam ta yi kira ga jama’a su daina mu’amala da mutanen da suke bin su suna karbar kudi daga hannunsu da sunan za su…

Hukumar Kwastam ta yi kira ga jama’a su daina mu’amala da mutanen da suke bin su suna karbar kudi daga hannunsu da sunan za su sayar musu kayan gwanjo na hukumar.

Kwamandan Hukumar Kwastam mai kula da jihohin Oyo da Osun, Kwanturola Abdullahi Zulkifili ne ya yi wannan kira a hira da ’yan jarida a ranar Talata da ta gabata a Ibadan. Ya ce, “Kamata ya yi mutane su rika ziyartar ofisoshinmu domin yin bincike a kan duk abin da ya shafi Kwastam domin irin wadannan mutane ’yan damfara ne babu ruwanmu da su.”

Wannan kira da Kwanturola Zulkifili ya yi ya biyo bayan daurin shekara 3 ba tare da zabin biyan tara ba da Babbar Kotun Tarayya ta Ibadan ta yanke wa wani mutum mai suna Bayo Mafo wanda aka same shi da laifin yin sojan gona ta hanyar sanya rigar sarki ta Kwastam yana karbar kudade daga hannun mutane yana yi musu alkawarin taimakonsu wajen sayen kayan gwanjo cikin sauki daga hukumar.

Yawan koke-koken jama’a mafi yawancinsu mata ne ya sa hukumar daukar matakin binciken lamarin da ya kai ga gano Bayo Mafo da aka kama shi aka gurfanar a  gaban kotu. “Mun yi matukar farin ciki da hukuncin kotun domin zai zama darasi ga mutanen da suke bata mana suna,” inji shi.

Ya ce yanzu haka hukumar ta kama mutum 8 da ake zargi da hannu wajen shigo da kayayyaki ta haramtacciyar hanya.

“Kotu ta bayar da belin mutanen amma lauyoyinmu suna ci gaba da tuhumarsu da laifin shigo da kayan da suka hada da motocin alfarma 8 da buhunan shinkafa 3,270 da jarkokin man girki 700 da dilolin gwanjo 20 da buhunan sukari 50 da suka kai na kimanin Naira miliyan 105 da muka kama a cikin wata uku na farkon bana,” inji shi.

Da yake nuna kayan ga ’yan jarida a Ibadan, Kwanturola Abdullahi Zulkifili wanda yake tare da Mataimakinsa, Tanko Bayero ya ce harajin fito na fiye da Naira biliyan 13 da hukumar ta tara a cikin wata 3 na farkon bana ya rubanya wanda aka tara a bara a daidai irin wannan lokaci. Ya jinjina wa takwarorinsa na jami’an tsaro na soja da ’yan sanda da DSS da NCDSC inda ya ce hadin kan da suke bayarwa ga hukumar ne ya kai ga samun wannan nasara. Ya ce sashen shari’a na hukumar ya gurfanar da mutum 8 gaban kotu bayan zarginsu da hannu wajen fasa kwaurin wadannan kaya.

Ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakan dakile ayyukan fasa kwauri da suke yin zagon kasa ga tattalin arziki. “Za mu ci gaba da yaki da masu fasa kwauri domin kare masana’antun kasar nan da farfado da wadanda suka durkushe wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga dimbin matasa tare da bunkasa tattalin arziki,” inji shi.