✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku daina garkuwa da mutane ko mu taru mu muku mummunar addu’a – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga masu mummunar dabi’ar nan,…

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga masu mummunar dabi’ar nan, ta garkuwa da mutane a kasar nan, su tuba su bari, ko kuma al’ummar kasar nan su taru su yi masu mummunar addu’a.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude wani sabon masallaci da aka gina, a Unguwar Zinariya da ke garin Jos.

Ya ce matasa kowa ya nemi sana’a su guji garkuwa da mutane, domin daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu an kashe daruruwan matasa masu irin wannan mummunar sana’a.

“Muna kira ga matasan da suka shiga wannan mummunar sana’a su tuba, su bari. Idan kuka ce ba za ku tuba ku daina ba, za mu hadu mu yi ta muku miyagun addu’o’i dare da rana.”

Sheikh Jingir ya yaba wa al’ummar wannan unguwa ta Zinariya, kan yadda suka yi gine-ginen gidaje a wajen.

Ya ce kamar shekara 22 da suka gabata ya bayar da shawarar cewa ya kamata mutane su je su sayi fili a wannan tsauni na Zinariya su gina gidaje.

Sannan ya yi kira ga al’ummar unguwar su taru su raya masallacin.

Shi ma da yake jawabi a wajen, Shugaban Majalisar Malamai reshen Unguwar Zinariya Alaramma Malam Abdurrahaman Ahmad ya bayyana cewa shi dai wannan sabon masallaci da aka gina, masallaci  ne na salloli guda 5 amma mai kama da masallacin juma’a, domin yana da fadi.

Tun da farko a nasa jawabin wanda ya gina wannan masallacin, Alhaji Umaru Zubairu Lalu ya yi godiya ga Allah da Ya ba shi damar gina wannan masallaci.

Sannan ya ce zai gina azuzuwan koyon karatun Alkura’ani a masallacin.