Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar da su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na N1,000 da N500.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
- Yanzu matsalar canjin kudi ba za ta shafi zabe ba – Shugaban INEC
- ISWAP ta sako ma’aikacin lafiyar da ta sace a Borno wata 11 da suka gabata
El-Rufa’i ya ce ya ba da umarnin ne la’akari da hukuncin da kotun Kolin Najeriya ta zartar kan ci gaba da amfani da su ba tare da wani kayyadajjen wa’adi ba.
Sanarwar ta ce, “La’akari da umarnin Kotun Kolin Najeriya, Gwamnatin Jihar Kaduna na umartar hukumomi da ma’aikatunta da su tabbata masu karbar kudadensu sun ci gaba da karbar kowanne nau’i na kudi, sabo da tsoho.
“Dokokin Jihar Kaduna ba su ba jami’an gwamnati damar karbar tsabar kudi a matsayin haraji ba. Amma jami’an da aka ba dama suna da hurumin karbar tsabar kudi idan bukatar hakan ta taso, kuma ana bukatar su bi wannan umarnin sau da kafa,” in ji sanarwar.
Ko a cikin makon nan sai da Gwamnan ya umarci mutanen Jihar da su yi watsi da umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Babban Bankin Najeriya (CBN) sannan su ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden.
A ranar Alhamis ce dai Shugaba Buhari yayin wani jawabi ya sanar da kara wa’adin ci gaba da amfani da takardar tsohuwar N200, har zuwa nan da 10 ga watan Afrilu mai zuwa, yayin da ya ce N1,000 da N500 kuma sun daina aiki.
Umarnin Kotun Kolin na farko dai na zuwa ne bayan wasu Gwamnonin Jihohi uku, cikinsu har da El-Rufa’i, sun maka Gwamnatin Tarayya a gabanta a kan batun.