Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya gargadi masu ayyukan ta’addanci da satar mutane su bar Jihar Adamawa ko su fuskanci hukuncin kisa.
A ziyararsa ga Gangwari Ganye, Alhaji Umaru Sanda ziyara a Karamar Hukumar Ganye, Fintiri ya ce gwamnatin jihar ba za ta saurara wa kowa ba ko wata kungiya mai alaka da garkuwa da mutane ko ayyukan ta’addanci a jihar.
- Maharan da suka je garkuwa da magidanci sun dauke matarsa
- Sandar Majalisa ta yi layar zana a Ogun
- An rage farashin Data da kashi 50 a 2020 a Najeriya
“Bari na sake maimaitawa, na sake fito da komai fili, idan ka san wani mai satar mutane ko mai alaka da su, to ko dai ya bar Jihar Adamawa lami lafiya ko kuma idan mun kama shi ya fuskanci hukuncin kisa.
“Cin kashin ya isa haka, ba za mu lamunci irin wadannan ayyukan ta’addancin a jiharmu ba da mutanen cikinta ke kaunar zaman lafiya.
“Gwamnatin Jiha tare da hadin guiwar hukumomin tsaro za su yi aiki tare da saraukuna da shugabannin al’uma wajen fatattakar ’yan ta’adda daga jiharmu,” inji shi
Ya ci gaba da cewa, duk wanda yaki jin wannan gargadin to ba shakka ba ya mai kaunar zaman lafiyar jama’a ba ne don haka shi ma ba zai zauna lafiya ba.