Wani yaro mai suna Haneef ya karyata mahaifiyarsa a yayin da yake amsa tambayoyi a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano.
Hakan dai ya wakana ne a yayin da ake gudanar da shari’a tsakanin mahaifi da mahaifiyar yaron a kan wasu kudi da yaron ya tsinta.
- Babu wata ɓaraka a tsakanina da Baffa Bichi — Abba Gida-Gida
- NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kudin Hajjin bana
Tun da farko mahaifin yaron mai suna Bashir Abdullahi ya kai kara gaban kotun, inda yake zargin matarsa Sadiya Yau da mahaifinta Alhaji Yau Kiri da cin amana da boye wasu kudi da dansa Haneef ya tsinta kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Lauyan mai kara, Bashir Mukaddam ya shaida wa kotun cewa, Haneef ya tsinci wasu bandira 50 na Dalolin Amurka a Tudun Fulani da ke unguwar Darmanawa a yankin Karamar Hukumar Tarauni.
“Sai matarsa Sadiya ta dauki kudin ta ba mahaifinta wanda shi kuma ya ce zai ajiye kudin tsawon shekara guda.
“Amma daga baya sai ya ci amana ya ruf da ciki a kan kudin ya kuma hana mai kara kasonsa.”
Shi ma a nasa jawabin, lauyan wadanda ake kara, Barista Abdurrahman Sulaiman ya musanta batun tsintar kudin, inda ya ce iya saninsu Haneef ya tsinci wata tsohuwar karamar jaka (wallet) inda mahaifiyarsa ta karba ta ajiye a daki.
“Lokacin da Haneef ya ba mahaifinsa labarin tsintuwar da ya yi sai ya sami matarsa ya tambaye ta ina jakar kudin da yaron ya tsinta, inda ita kuma cikin mamaki da wasa ta ce masa ta kai wa mahaifinta.
“Tun daga wannan lokaci ba a sake yin maganar ba har zuwa lokacin da aka fara juya maganar a dangi.”
Wakiliyarmu da ta halarci zaman kotun, ta ruwaito cewa Haneef ya tabbatar da cewa lallai ya tsinci kudi kuma ya damka wa mahaifiyarsa.
Sai dai ya gaza tantance irin kudin da ya tsinta don haka kuma ya gaza bayyana adadin yawan kudin da ya tsinta.
Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya bayyana cewa kotun ba za ta yi amfani da shaidar yaron ba kasancewar yana da karancin shekaru wanda ba ya iya bambance abubuwa da dama.
A karshe dai kotun ta umarci wadanda ake kara da su yi rantsuwa da Alkurani mai girma, inda bayan sun rantse ne kotun ta rufe shari’ar gaba daya.