Rahoton da kafar watsa labarai ta Naijanews ta kalato ya nuna cewa kowane kulob daga cikin 16 da za su fafata a zagaye na biyu na Gasar Zakarun Kulob na Turai ya samu kyautar Fam miliyan 8 wanda ya yi daidai da Naira biliyan 3 da miliyan 816.
Idan za a tuna kungiyoyi 16 ne suka kai wannan matsayi inda aka fitar da jadawalinsu a ranar Litinin da ta wuce.
Kungiyoyi 8 da suka haye zuwa mataki na gaba za su sake samun wata kyauta daga hukumar shirya gasar har zuwa matakin karshe.