Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce jam’iyyarsu ta PDP na da kwararan hujojjin da suke tabbatar da cewa dan takararsu Atiku Abubakar ne ya lashe zaben Shugaban Kasa na 2019.
Gwamnan ya ce shugaba Buhari ya san cewar bai ci zabe ba, amma an shirya wata makarkashiya ce wacce aka yi amfani da ita wajen kayar da dan takarar nasu, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa a zaben da ya gabata.
- Matan gwamnoni sun ba matan da aka yi wa fyade a Zamfara tallafi
- Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika
- Malaysia ta ba jakadun Koriya ta Arewa sa’o’i 48 su fice daga kasarta
- Mahara sun yi awon gaba da matar Dagaci a Kebbi
Gwamnan Bala na wadannan kalaman ne a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels, a daren ranar Alhamis.
A cewarsa, “Muna da hojojji da suka nuna yadda jami’an tsaro da Hukumar Zabe suka hade kai a yayin zaben 2019.
“Na tabbata ‘yan Najeriya ba su manta abubuwan da suka faru a zaben ba, amma jam’iyyar PDP ta koyi darasi kan lamarin.
“Ba za mu sake bari abin da aka yi a zaben baya ya sake faruwa ba, za mu tabbatar da cewa mun toshe dukkan kafar yin magudi a zabe mai zuwa,” cewar Gwamnan.
Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) dai ta ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben a wancan lokacin, ko da yake PDP da dan takarar nata sun kalubalanci zaben har zuwa Kotun Koli amma a can ma suka yi rashin nasara.