✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kowa na iya kamuwa da cutar shanyewar barin jiki ba sai manya ba’

'Yanzu ba sai wadanda suka manyanta ba ne kawai za su iya kamuwa da cutar'

Sabanin yadda tunanin jama’a yake a baya kan cutar shanywar barin jiki, inda ake ganin sai masu yawan shekaru ne kadai kan yi fama da ita, yanzu an tabbatar cewa kowa na iya kamuwa da ita.

Kungiyar nan mai zaman kanta, Stroke Action, ta ce cutar shanyewar barin jiki cuta ce da kowa zai iya kamuwa da ita ba wai sai dattawa kadai ba.

Don haka kungiyar ta ce akwai bukatar wayar da kan jama’a dangane da wannan cuta, kama daga abin da ya shafi alamominta zuwa yadda za a yi maganinta idan an kamu da ita.

A cewar babbar jami’a a kungiyar, Rita Melifonwu, wannan cuta na iya kama kowa, a ko’ina kuma a kowane lokaci.

Rita ta yi wadannan bayanan ne albarkacin bikin Ranar Yaki da Cutar Shanyewar Jiki ta Duniya wanda aka saba yi ranar 29 na Oktoban kowace shekara.

Kungiyar ta ce cikin duk mutum hudu akan samu mutum guda da zai kamu da wannan cuta a rayuwa.

Ta kara da cewa, adadin masu kamuwa da cutar ya karu da kashi 50 cikin 100 a tsakanin shekara 17 da suka gabata.

Ta ce, kashi 63 na wadanda suka yi fama da cutar a 2019, mutane ne ‘yan kasa da shekara 70.

“Mutum miliyan 12.2 ne kan kamu da wannan cuta duk shekara a fadin duniya, mutum daya cikin kowane dakika uku, yayin da take kashe mutum miliyan 6.5 duk shekara a fadin duniya,” inji Rita.

Rita ta ce akwai bukatar jama’a su ba da muhimmanci zuwa duba lafiyarsu a asibiti, saboda a cewarta, cutar na daga cikin cututtukan da ke kan gaba wajen kisa a duniya.

(NAN)