Dan wasan kungiyar West Ham Kourt Zouma wanda tsohon dan wasan Chelsea ne na iya fuskantar cin sarka bayan wani bidiyonsa ya bulla wanda ya nuna yana bugun kyanwarsa a gidansa da ke Ingila.
A cikin bidiyon, dan wasan na Faransa mai shekara 27 ya bi kyanwar da gudu shi kuma wanda yake nadar bidiyon yana dariya.
- Ta’aziyyar Hanifa da Ahmad Bamba ta kai Aisha Buhari Kano
- Za a binciko yadda aka shigo da gurbataccen man fetur Najeriya
Hakan kuma bidiyon ya nuna lokacin da yake jifan kyanwar da takalminsa sannan a karshen bidiyon aka gan shi yana marin kyanwar.
Tuni dai kungiyar West Ham ta sanar ta cin tarar dan wasan Dala 250,000, inda kungiyar ta ce za ta bai wa Kungiyar Jinkan Dabbobi kudin.
Kamfanin Adidas mai daukar nauyin takalmin taka ledan dan wasan ma sun yanke alaka da shi saboda bidiyon.
Haka kuma kamfanin Bitality UK da ke daya daga cikin kamfanonin da ke daukar nauyin kungiyar sun sanar da daina alaka da kungiyar, sannan kamfanin Experience Kissimmee da Yield App suka ce suna bin diddigin lamarin ne kafin su yanke shawara.
Tuni dan wasan ya fitar da sanarwar bayar da hakuri, amma hakan bai hana shi shan suka ba, musamman bayan da magoya bayan kungiyar ta West Ham suka rika yi masa ihu a wasansu na karshe.
A sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa ya yi da-na-sanin abin da ya aikata, sannan ya ce kyanwar na nan cikin koshin lafiya, kuma su biyu ne kuma yana matukar kaunarsu, sannan ya ce ya amince da tarar da kungiyarsa ta West Ham ta yi masa yana mai bayar da hakuri.
Ana tunanin dan wasan mai darajar Dala miliyan 30 ya yi wa kyanwar hukuncin ne bayan ta yi barna a cikin gidan.
Kanin dan wasan mai suna Yoan ne ya sa bidiyon a kafar Snapchat, sannan ya biyo shi da alamar dariya, yanayin da ke nuna nishadi.
Rundunar ’yan sandan Essed ta fara binciken lamarin, sannan kungiyoyin Jinkan dabbobi a Ingila da Faransa sun shiga lamarin da nufin kotu domin kwato wa kyanwar hakkinta.
Sai dai kungiyar Jin Kan Dabbobi sun yi Allah wadai da dan wasan inda Kakakinta ya ce, “abin takaici ne kallon bidiyon.
“Ba daidai ba ne mutum ya mari dabba ko duka a matsayin hukunci ko wani abu.”
Dokta Maggie Roberts ta Kungiyar Jinkan Kyanwowi ta ce duk wanda aka gani yana cin zarafin dabba a kawo musu kararsa, kuma suna aiki tare da ’yan sanda.
A wata doka da The Sun ta kalato, kafar ta ce a sabuwar dokar da aka amince a bara a majalisar kasar, yanzu za a iya kulle mutum har na tsawon shekara biyar, maimakon wata shida na da.
Kungiyar West Ham ta kuma sanar da cewa za ta ba kungiyar dabbobin hadin kai domin gudanar da binciken da ya kamata.
Sannan akalla mutum 80,000 suka nuna bukatarsu ta a hukunta dan wasan.
A Faransa ma lamarin ya dau zafi, inda Gidauniyar 30 Millions Friends Foundation ta dauki lauya domin zuwa kotu.
Tuni gidauniyar ta gabatar da karar dan wasan a Paris.
Kakakin gidauniyar ya ce suna bukatar a dakatar da dan wasan da buga wa kasar Faransa.
A dokar Penal Code ta Faransa, duk dan kasar da aka samu da laifin cin zarafin dabba zai iya fuskantar zaman gidan yari har na tsawon shekara hudu.