Barista Lawal Ishak, lauya ne mai zaman kansa da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.
A tatattaunawa da wakilinmu, kan yadda aka gudanar da shari’o’in zabubbukan jihar, ya ce Kotun daukaka kara da Kotun koli ne kadai, za su warware shari’o’in zababbu.
- Sauke hadiman Gwamnan Kano da siyasar da ke ciki
- An kashe dalibi saboda budurwa a Jami’ar FUDMA da ke Katsina
Yaya kake ganin yadda kotunan sauraron kararrakin zabe, suka gudanar da shari’o’in zabubbukan da suka gabata a Jihar Filato?
A fahimtata ta masanin shari’a, na san cewa shari’a sabanin hankali ce. Duk da cewa wani lokaci akan duba shari’a ne kan yadda ta zo. Wato yadda ka gabatar da bayani ga kotu, haka za ta karba, kuma ta yanke hukunci kan bayanin da ka gabatar mata.
Akwai abin da ya faru a shari’o’in zabubbukan Jihar Filato. Yawaicin kararrakin zabubbukan, an yi su ne kan Jam’iyyar PDP.
Kuma jam’iyyun da suka shigar da kararrakin uku ne, wato APC da yanzu ta zama ta adawa a jihar da Jam’iyyar LP da Jam’iyyar PRP.
A hukuncin farko da aka fara yankewa, na kujerar dan Majalisar Wakilai, mai wakiltar Mazabar Jos ta Arewa da Bassa da dan takarar Jam’iyyar PRP da ya zo na biyu a zaben, ya shigar da Jam’iyyar PDP da dan takararta.
A karar da dan takarar PRP ya shigar, ya ce bai kamata Jam’iyyar PDP ta shiga zaben ba. Saboda lokacin da aka yi zaben cike-gurbi a mazabar, a shekarar 2021, wannan dan takara na Jam’iyyar PRP ya kai karar PDP, inda kotun ta tabbatar da cewa Jam’iyyar PDP ba ta da ikon shiga zaben, saboda ta ki bin umarnin da kotu ta ba ta na ta je ta gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar.
A lokacin Kotun Sauraron kararrakin Zabe ta yanke hukumci kan haka. Jam’iyyar PDP ta daukaka kara, a can ma Kotun daukaka kara ta tabbatar cewa Jam’iyyar PDP ba ta da damar shiga zaben. Saboda haka, aka bai wa dan Jam’iyyar PRP, wanda shi ne ya zo na biyu a zabe.
Amma a wannan karo da aka shigar da kararraki, tun daga na kujerun Majalisar Dokokin Jihar da na tarayya da na Gwamna cewa Jam’iyyar PDP ba ta da damar tsayawa takarar zabe, abin mamaki, hukuncin da aka fara yanke wa shi ne na dan takarar Jam’iyyar PRP. A hukuncin sai kotun ta nuna cewa ta gamsu cewa Jam’iyyar PDP ta yi zaben shugabannin jam’iyyar. Saboda haka, ta kori karar.
Kuma abin sha’awa shi ne alkalan da aka turo Jihar Filato, don gudanar da wadannan shari’o’i guda 6 ne ko 7. Sai suka raba kansu gida biyu, don su yi saurin gudanar da wannan aiki, wato kotu ta daya da kotu ta biyu.
Da aka zo sauraron kararrakin kujerun sanata da na ’yan Majalisar Tarayya na Jos ta Kudu da Jos ta Gabas da Barikin Ladi da Riyom, sai kotu ta biyu ta ce PDP ta saba ka’ida sai ta soke zaben da aka ce PDP ta ci.
A nan tsohon Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya samu nasara a kujerar Sanatan Filato ta Kudu. Sauran kujerun kuma aka bai wa ’yan takarar APC da LP.
Abin da ya bai wa mutane mamaki, shi ne abubuwa sun gudana, kuma iri daya ne. Amma alkalai kashi biyu, kowa da wajen da ya fuskanta.
A kotun farko alkalan sun ce Jam’iyyar PDP ba ta da laifi. A kotu ta biyu kuma alkalan sun ce PDP ta yi laifi, don haka suka soke zabubbukan da ta ci.
Maganar da ake yi tun da farko, ita ce a lokacin da Jam’iyyar PDP ta shirya zaben shugabanninta a Jihar Filato. Sai wani tsohon dan Majalisar Wakilai na mazabar Jos ta
Kudu da Jos ta Gabas mai suna Bitrus Kaze ya yi korafi, inda ya shigar da kara a Babbar Kotun Jos cewa an yi daukidora ne a zaben. Wannan kotu, ta ce wannan korafi gaskiya ne, don haka ta bai wa PDP umarnin ta je ta sake zaben na shugabanninta.
Jam’iyyar PDP, ba ta sake wannan zabe ba. Sakamakon haka, aka hana jam’iyyar shiga zaben shugabannin kananan hukumomin jihar da aka gudanar a shekarar 2021.
PDP ta daukaka kara, kan hukunci, a Kotun daukaka kara ta Jos. A wannan kotu ma, aka yanke hukunci cewa matakin da Hukumar Zabe ta Jihar ta dauka na hana PDP shiga zaben ya yi daidai.
To a kan wannan al’amari alkalan kotunan sauraron kararrakin zaben Jihar Filato suka rabu biyu. Wasu suna cewa PDP ba ta bi umarnin kotu ba, don haka ba ta da damar shiga wadannan zabubbuka. Wasu kuma suka ce Jam’iyyar PDP ta bi umarnin kotu, don haka tana da damar shiga zaben.
A bangaren shari’ar zaben Gwamna, magoya bayan Jam’iyyar APC suna cewa ba a yi masu adalci ba. A yayin da a bangaren shari’o’in kujerun majalisa, magoya bayan PDP suna cewa ba a yi masu adalci ba, me za ka ce?
Ya danganta ga yadda mutum ya dubi wadannan abubuwa. A sanina dai na fahimci cewa ita PDP a kan shari’ar da ta yi tsakaninta da Hukumar Zabe ta Jihar Filato, wanda kotu ta ce ta yi daidai da ta hana ta shiga zabe.
Kuma PDP ta daukaka kara, Kotun daukaka kara da ke nan Jos ta ce hukumar zaben ta yi daidai. Don haka, kotun ta kori karar.
Jam’iyyar PDP ta daukaka kara zuwa Kotun koli kan hukunci, amma ba su kula wannan kara ba, har sai da aka zo gab da zaben da ya gabata.
To ka ga tunda an kori wannan kara, hukuncin daukaka karar shi ne yake aiki. Kuma hukunci ya ce PDP ba ta yi zaben shugabannin jam’iyyar ba, saboda haka, ba ta da halattattun shugabanni, don haka ba ta da damar shiga wadannan zabubbuka.
To abin da ya kawo takaddama a zaben Gwamna, shi ne su shugabannin Jam’iyyar PDP suna cewa sun yi zaben shugabanninsu, a ranar 25 ga watan Satumban bara.
Wasu suna ganin idan sun yi wannan zabe, me ya sa ba su gabatarwa Kotun kolin ba? Wannan ya sa wasu suke ganin akwai rashin adalci a wajen wadannan alkalai uku na Kotun Sauraron kararrakin Zabe da suka yanke hukunci kan zaben Gwamnan Filato.
Kamar yadda na fada ne tunda farko shari’a tana da irin wannan yanayi. Kowa da inda yake kallo. To amma dama amfanin Kotun daukaka kara ke nan, ta duba ta ga wane ne ya yi daidai, wane ne kuma bai yi daidai ba.
PDP tana korafin cewa ta bi ka’ida kan umarnin da kotu ta ba su na su je su yi zaben shugabanninsu. Kuma suka ce sun yi wannan zabe a ranar 25 ga Satumban bara, don haka ta ce ba a yi mata adalci ba.
Su kuma jam’iyyun adawa na APC da LP suka ce PDP ba ta yi wannan zabe ba. Suka ce PDP ta yi zabe a kananan hukumomi 6 ne kawai, maimakon 17 na jihar.
Kowa da inda ya dage kan wannan dambarwa. Don haka kamar yadda na fada kotunan gaba ne za su warware wannan dambarwa.
Yaya kake ganin yadda siyasar Jihar Filato za ta kasance nan gaba, sakamakon shari’o’in zabubbukan da aka yanke?
Wannan al’amari ba zai shafi siyasar Jihar Filato sosai ba. Dalili kuwa shi ne kowa ya kalli yadda aka gudanar da zabubbukan da suka gabata.
Za a ga cewa addini ya taka rawa sosai. A Jihar Filato, wasu al’ummomi musamman mabiya addinin Kirista, sun dauki Jam’iyyar PDP kamar addini.
Suna ganin cewa ita ce za ta share masu hawaye, a matsayinsu na mabiya addinin Kirista. Kuma suna ganin Jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya ce ta Musulmi zalla.
Wannan ya yi tasiri sosai a zaben da ya gudana. Domin idan ka bibiyi wannan zabe da aka yi a nan Filato, za ka ga cewa a zaben Shugaban kasa al’ummar Filato ba su zabi Jam’iyyar APC ba.
Kuma ba su zabi PDP ba, saboda suna ganin dukkan ’yan takarar jam’iyyum Musulmi ne. Don haka, sai suka zabi Jam’iyyar LP wadda dan takarar ta Peter Obi, Kirista ne.
Da aka zo zaben Gwamna, nan kuma sai suka ki zaben jam’iyyun APC da LP suka zabi PDP. Su kuma al’ummar Musulmin Jihar Filato sun fi karkata ne ga Jam’iyyar APC a zabubbukan da aka yi.
Ba ina nufin babu Musulmi a cikin PDP ba ne, haka kuma ba ina babu Kiristoci a APC ba ne. Amma a kullum idan ka kalli mutumin Filato yana kallon Jam’iyyar PDP ce ya kamata ya yi.
Domin a ganinsa ita ce ta yi daidai da addininsa na Kirista. To ka ga su a ganinsu haka ya yi daidai. Domin kafin yanke hukuncin, an samu raderadin cewa za a iya samun tashin hankali, ganin yadda aka yi shari’ar zaben Gwamna Kano aka kwace aka bai wa Jam’iyyar APC.
Da yawa an tsorata, saboda an kwace zaben Sanata na Filato ta Kudu daga wanda ya ci aka bai wa tsohon Gwamnan Jihar Simon Lalong na APC.
Sai aka yi zaton za a iya kwace zaben Gwamna, kuma aka rika rade-radin cewa idan aka kwace za a iya samun tashin hankali. Amma daga baya da ba a kwace ba, sai aka ji shiru.
Sai dai ba mu san yadda za ta kaya a Kotun daukaka kara da ke nan Jos ko kuma Kotun koli da ke Abuja ba.
Mene ne sakonka ga al’ummar Filato, kan wadannan shari’o’i da aka gudanar?
Sakona ga al’ummar Filato guda daya ne, mu yarda ita dimokuradiyya dama ce da kowane dan Adam yake samu. Idan ba ka samu dama a wannan karo ba, ka yi hakuri ka jira wani lokaci ya zo, domin ka kara gwada kokarinka. Kuma ya kamata jama’a su fahimci cewa ba dole ne wanda mutum ya zaba ya kasance ya ci zabe ba.