Wanda ya kafa Jam’iyyar NNPP, Boniface Aniebonam ya shirya taron addu’a ta musamman domin rokon nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Koli.
Boniface Aniebonam ya shaida wa mahalarta taron addu’ar cewa ba shi da matsala da dan takarar shugaban kasa na jam’ittar a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, amma Gwamna Abba ne jagoran jam’iyyar a Jihar Kano.
Ya ce a bisa doka da kuma tsarin jam’iyya, Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne jagoran NNPP a Jihar Kano, kuma “Muna ganawa da Gwamnan Abba, shi ya ma muka shirya wannan taron addu’ar.”
Aniebonam wanda shi ne shugaban Kungiyan Masu Fion Kaya na Kasa (NAGAFF), ya jagoranci kungiyar wajen gudanar da addu’ar ganin lokacin shari’ar zaben Gwamnan Kanon na kara matsowa.
Idan za a iya tunawa, Kwamitin Gudanawan NNPP na Kasa da ke tsagin tsohon Gwwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’ittar a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dakatar da Boniface Aniebonam daga jam’iar.
Amma da yake jawabi a taron addu’ar, Aniebonam ya ce babu baraka a NNPP, hasali ma, shi da Kwanwkwaso babu wanda ya yi magana kan rikicin shugabanci a jam’iyyar.
“Sannan kuma ba ni da wata da Kwanwkwaso,” in ji shi, yana mai cewa wasu abubuwan da ke faruwa a NNPP aikin “an baranda ne domin samun wani abu daga iyayen gidansu.
Za a iya tunawa cewa kotun daukaka kara ta tarayya ta tabbatar da hukuncin kotun shari’ar zabe da ta kwace kujerar Abba Kabir Yusuf, gwamna daya tilo da NNPP ke da shi a fadin Najeriya.