Kotun Koli ta yi watsi da bukatar da aka gabatar mata ta sake nazari a kan hukuncin da ta yanke wanda ya nuna ‘yan takarar jam’iyyar APC a zabukan 2019 na jihar Zamfara ba su cancanta ba.
Hudu daga cikin alkalan kotun su biyar ne a karkashin jagorancin Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad, suka yi ittifaki ranar Juma’a cewa bukatar mummunan karan-tsaye ne ga dokokin Kotun.
Alkalan hudu, wadanda Mai Shari’a John Inyang Okoro ya karanta matsayarsu, sun umarci bangaren Abdulazeez Yari ya biya bangaren Kabiru Marafa Naira miliyan biyu.
Sai dai alkali na biyar, Mai Shari’a Chima Nweze, na da sabanin ra’ayi; a hukuncinsa, ya ce shi ya amince da sake duba hukuncin saboda bai kamata Kotun Kolin ta bai wa PDP nasara kyauta duk da cewa ba ita a cikin wadanda ke karar juna.
A watan Fabrairu ne dai Mai Shari’a Tanko Muhammad ya sauya fasalin tawagar alkalan za ta saurari bukatar da wasu ‘yan jam’iyyar APC a Zamfara suka gabatar suna kalubalantar hukuncin Kotun Kolin.
Wadanda suka gabatar da bukatar dai su ne bangaren tsohon Gwamna Abdulaziz Yari.
Kotun Kolin dai ta yanke hukuncin cewa wadanda suka shigar da karar ba su da madogara ne bisa hujjar cewa jam’iyyar ta APC ba ta yi zaben fitar da gwani ba.