✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotun Koli ta yi fatali da bukatar Buhari ta sauya Dokar Zabe

Buhari ba shi da hurumin neman a soke dokar da ya riga ya amince da ita.

Kotun Koli ta yi fatali da wata bukata wadda Shugaba Muhammadu Buhari da Antoni Janar Abubakar Malami suka shigar suna nema ta soke Sashe na 84, karamin sashe na 12 cikin baka na Dokar Zabe ta 2022.

Kotun ta ce Shugaban kasar ba shi da hurumin neman a sauya dokar da ya riga ya amince da ita, sannan ta kwatanta bukatar tasa da yi wa tsari na shari’a karan tsaye.

Sashen ya haramata wa duk wani mai rike da mukami na siyasa, da aka nada a dukkan matakai, ya kada kuri’a a zaben fitar da gwani na duk wata jam’iyya.

Alkalan Kotun bakwai da suka yi zaman ranar Juma’a a karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.

A hukuncin da Mai Shari’a Akomaye Agi ya karanto, Kotun Kolin ta ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 da Dokar Zabe 2022, bayan da a baya ya aminta da shi.

“Shugaban kasar ba shi da ikon bukatar majalisa ko tursasa ta ta sauya wani abu a dokar da a baya ya bada hadin kai ya kuma aminta da shi,” in ji shi.

Karar ta biyo bayan hukuncin wata kotu a birnin Umuahia a jihar Abia, wadda ta soke sashe na 84 (12) karamin sashe na 122.

Ana iya tuna cewa bayan gabatar masa da kudirin, Shugaba Buhari ya yi korafi a kan wannan batu, amma ya sanya hannu daga bisani bisa tunanin cewa majalisa za ta cire sashen daga dokar.