✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da Oborevwori a matsayin gwamnan Delta

Kotun ta amince da hukuncin da kotunan kasa suka yanke, na tabbatar da Oborevwori a matsayin gwamnan jihar.

Kotun Koli da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da karar soke zaben Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan Jihar Delta.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce, ta ayyana Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Sai dai jam’iyyu uku ba su gamsu da sakamakon zaben ba, inda suka garzaya kotu domin neman a soke nasarar gwamnan.

Tun da farko, Oborevwori ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara.

Kazalika kotun koli, ta amince da hukuncin da kotunan kasa suka yanke tare da tabbatar da nasarar Oborevwori a zaben gwamnan Jihar Delta.

Kotun ta yi watsi da karar Ovie Omo-Agege ya shigar na neman soke zaben Gwamna Oborevwori.

Kotun kolin ta ce wanda ya shigar da karar ya gaza tabbatar da batun aringizon kuri’a da kuma rashin bin dokokin zabe.

Haka kuma ta yi watsi da batun rashin cancanta tare da tabbatar da zaben Oborevwori na jam’iyyar PDP.

Sai dai kotun ba ta sanya wa wadanda suka shigar da kara tara ba.