Kotun Koli ta tabbatar da zaben Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Zamfara.
Kotun Kolin ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wadda ta bayyana zaben gwamnan a matsayin wanda bai kammala ba, kuma ta bayar da umarnin sake zabe a wasu kananan hukumomi uku na jihar.
Hukumar zaɓe dai ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.
Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi INEC da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.