Kotun Koli ta soke dokar da ta haramta wa dalibai Musulmi sanya hijabi a makarantu a Jihar Legas.
Kwamitin Alkalai shida na Kotun Kolin ne ya yanke hukuncin a zaman kotun na ranar Juma’a, ya kuma bayyana cewa umarnin ya takaita ne a makarantun gwamnatin jihar.
- Yadda rashin wutar lantarki ke durkusar da masana’antu a Kano
- Batanci ga Annabi: Shugabannin Musulman Indiya sun bukaci dakatar da zanga-zanga
Alkalan sun bayyana haramta wa dalibai Musulmi ’yancinsu na sanya hijabi a matsayin tauye hakkinsu na yin addini da tsare mutuncinsu a matsayinsu na ’yan Adam da kuma walwalarsu, sabanin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Wannan hukunci dai ya sanya farin ciki da murna a zukatan al’ummar Musulmi, inda Shugaban Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) Reshen Jihar Legas, Miftahudeen Thanni tare da mambobin kungiyar suka yi ta kabbara tare da hamdala.
Alkalan da suka yanke hukuncin su ne Mai Shari’a Olukayode Ariwoola da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun da Mai Shari’a John Inyang Okoro da Mai Shari’a Uwani Aji da Mai Shari’a Mohammed Garba da Mai Shari’a Tijjani Abubakar da kuma Mai Shari’a Emmanuel Agim.
A hukuncin da ta yanke da farko, kotun daukaka karar ta bayyana cewa hana dalibai Musulmi sanya hijabi ba komai ba ne face nuna musu wariya.