Kotun Kolin Najeriya ta sanya ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba domin sauraron karar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
- Tinubu ya janye nadin da ya yi wa matashi mai shekara 24 a shugabancin FERMA
- Tinubu ya nada sabbin shugabannin NTA, NAN da NBC
Amma, Atiku, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben ya garzaya gaban kotun sauraron kararrakin zabe yana kalubalantar nasarar ta Tinubu, amma ta yi watsi da karar.
Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar na Najeriya ya sake garzayawa gaban Kotun ta Koli inda ya bukace ta da ta jingine hukuncin kotun ta baya, saboda a cewarsa, kotun baya ba ta yi la’akari da batutuwan da ya gabatar a matsayin hujjoji a gabanta ba.
Atiku dai takamaimai na son Kotun Kolin ta yi la’akari da zargin gabatar wa INEC takardun bogi da yake zargin Tinubu ya yi gabanin zaben domin ta kwace nasararsa, ta ba shi.