✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotun Koli ta dage sauraron shari’ar Canjin Kudi

Kotun Koli ta sanya 3 ga watan Maris, 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari'ar

Kotun Koli ta sanya 3 ga watan Maris, 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari’ar da ke kalubalantar dokar sauyin kudi da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Alkalan Kotun su bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro sun sanar da haka ne a zaman kotun na ranar Laraba.

Daga nan suka dage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Maris mai kamawa.