Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni suka shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.
Gwamnonin Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara ne dai suka garzaya kotun suna neman a hana bankin daina amfani da tsoffin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200 daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun dai, a yayin zamanta na ranar Laraba ta dage ci gaba sauraron karar har zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairin 2023.
Tun farko dai CBN ya sanya 31 ga watan Janairu a matsayin ranar daina amfani da tsofaffin takardun kudin, kafin daga bisani ta kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.
Sai dai gabanin cikar wa’adin, Jihohin uku suka bukaci Kotun Kolin ta hana CBN ci gaba da daina karbar kudaden.
Daga nan ne kotun ta amince da bukatar tasu, sannan ta dage ranar ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu.
Daga bisani dai Jihohin Ribas a Kano su ma sun nemi su shigar da makamanciyar wannan karar a daidaikunsu, suna kalubalantar Gwamnatin Tarayya da fara amfani da manufar ba tare da samun amincewar Majalisar Zartarwa da kuma ta Magabatan Kasa ba.
Amma daga bisani kotun ta umarce su da su hade tasu da wacce ta fara saurara, tun da dama ta fara sauraron ta, sannan ta sanya ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu mai zuwa don sauraron karar.