Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 9 ta yankewa wani tsohon dan Hisba, Dayyabu Muhammad, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun, wacce ke karkashin Mai Shari’a Amina Adamu, ta samu tsohon ma’aikacin Hisbar ne da laifin kisan bazawararsa mai suna Hauwa Ibrahim, laifin da ta ce ya saba wa sashe na 221 na Kundin Penal Code.
- Kasar Netherland za ta nemi afuwa kan cinikin bayin da ta yi a baya
- Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano
Aminiya ta rawaito cewa, Dayyabu tsohon ma’aikacin Hisba ne kuma ya kasance almajirin gidan su Hauwa, inda ya nuna ra’ayinsa na aurenta, har suka fara soyayya.
Daga bisani Dayyabu ya yi maganar auren, amma iyayenta suka ce ba su yarda da tarbiyyarsa ba, don haka ba za su ba shi ’yarsu ba.
Daga baya ita ma Hauwa ta nuna ba ta ra’ayinsa.
Hakan ne ya fusata Dayyabu inda ya je har gida a shekarar 2011 ya samu marigayiyar tana kwance a daki ya ce ya zo ne su yi sallama.
Nan take ya dauko wuka ya fara caccaka mata a ko ina na jikinta, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarta.
Da take zartar da hukuncin, Mai Shari’a Amina Adamu ta bayyana cewa ta yi amfani da gamsassun hujjoji da masu gabatar da kara suka gabatar wanda hakan ya tabbatar an kama wanda ake tuhuma da laifi nan take kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.