✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kano ta tisa keyar matashin da ya kashe mahaifiyarsa zuwa kurkuku

Kotun Majistare ta Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai kimanin shekaru 22 bisa zargin sa da laifin kisan mahaifiyarsa ’yar kimanin…

Kotun Majistare ta Jihar Kano ta tsare wani matashi mai kimanin shekaru 22 bisa zargin sa dalaifin kisan mahaifiyarsa ’yar kimanin shekaru 50 da haihuwa.

Tun da farko mai gabatar da kara Barista Rabia Saad ta shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya daba wa mahaifiyarsa wuka a duk ilahirin jikinta lamarin da ya janyo aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da shi na kisan kai wanda ya saba da sashe na 221 na Kundin Shari’ar Pinal Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Kofar Mata ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali inda kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Yuni, 2023.