Wata Babbar Kotun Majistare a Jihar Kano ta tsare wasu mutum tara a gidan kaso bisa zargin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
’Yan sanda sun gurfanar da mutanen ne bisa zargin hada baki, fashi da makami, mallakar makami ba bisa ka’ida ba da kuma satar mutane.
Alkalin kotun, Muhammad Jibrin ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin har zuwa lokacin da Ofishin Babban Mai Shigar da Kara na Jihar zai kammala tattara bayanai.
Daga nan sai ya dage sauraron karar zuwa 30 ga watan Satumba domin.
Tun da farko dan sanda mai shigar da kara, Isfekta Pogu Lale ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne ranar 10 ga watan Yuli a garin Kwanar Dangora na Karamar Hukumar Kiru.
Pogu ya ce wadanda ake zargin sun dauki bindigogi, adduna, sanduna kafin su kai wa wanda ke karar mai suna Abdulhadi Ahmed hari a gidansa.
Jami’in ya ce sun kwaci tsabar kudi N400,000 da mota kirar Peugeot da darajarta ta kai Naira miliyan daya da dubu 600.
Ya kara da cewa sun kuma sace Abdulhadi tare da karbar Naira miliyan daya a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta dukkannin zarge-zargenda ake tuhumarsu da aikatawa.