Kotu a Birtaniya ta yanke wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari.
Kotun ta daure Ekweremadu da matarsa, Beatrice ne bayan samunsu da laifin safarar sassan jikin dan Adam.
- An cafke matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Kano
- Allah Kadai Ya san jam’iyyar da zan mika wa mulkin Kano —Ganduje
Kotun ta samu Ike Ekweremadu da matar tasa da likitansu, Obinna Obeta, kan hada baki da yin safarar wani matashi daga Najeriya zuwa Birtaniya domin amfani da kodarsa.
Kotun da ke zamanta a Old Bailey na kasar Birtaniya ta kama ma’auratan da likitan nasu da laifin hada baki da nufin girbar kodar matashi, wanda ta ce nau’i ne na bauta.
Ma’auratan dai sun bayyana wa kotun cewa suna neman kodar da za a dasa wa ’yar shekara 25 mai suna Sonia mai fama da lalurar ciwon koda ne.
Dokta Obeta kuma zai yi shekara 10 saboda shi ne ya samo matashin ya da kuma amfani da rauninsa domin ciri kodar tasa.
Amma ita Beatrice mai shekara 56, shekara hud da wata shida za ta yi, saboda rawar da taka ba ta kai ta mijinta da likitan ba, kamar yadda akalin ya bayyana a zaman kotun da aka nuna a talabijin.