Wata kotun kasar Indiya ta yi watsi da bukatar wasu Musulmai da ke neman ta hana mabiya addinin Hindu damar yin bauta a jikin wani masallacinsu da aka gina tun a karni na 17.
Masallacin na Gyanvapi mai tsohon tarihi, tun zamanin daular sarki Mughal aka gina shi, kuma yana daf da wurin bautar addinin Hindu na Varansi Kashi Vishwanath da ke Arewacin jihar Uttar Pradesh.
- Lata Mangeshkar: Fitacciyar mawakiyar India ta rasu
- Motar bas makare da ’yan sanda ta fada kogi a indiya
Matan su biyar sun shigar da kara ne Kotun inda suke neman ta ba su izinin gudanar da ibadunsu a kullum, a wurin butar, kuma kotun ta amince, duk da kalubalantar da Musulman suka yi.
Kungiyar Musulman na kafa hujja ne da cewa dokar kasar ta wuraren ibadu ta shekarar 1991 ta tabbatar da cewa kowa ya tsaya a matsayinsa wanda hakan ya hana musu amfani da wurin, kamar yadda dokar ‘yan mulkin mallaka ta 15 ga watan Agustan 1947 ta ayyana.
Su kuwa mabiya addinin na Hindu na ikirarin cewa an gina masallacin ne a shekarar 1669 a bisa umarnin sarkin daular Mughal bayan an rushe wurin bautarsu da ke wurin tun asali.
Sannan sun ce har yanzu akwai gumakansu da sauran birbishin abubuwan butarsu a wurin.
Ikirarin da kungiyar Musulman da jami’an masallacin suka musanta, sannan ta kuma ce za ta daukaka kara a wata babbar Kotu da ke Allahabad, a hirarsu da Al Jazeera.