Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta biya CFA 7,564,250 ga iyalan tsohon shugaban kasar na mulkin soji, Janar Ibrahim Bare Mainasara, wanda aka yi wa kisan gilla.
Kotun ta kuma ba wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar wa’adin mako biyu ta gabatar mata shaidar yunkurin fara biyan kudaden ga magadan Janar Bare Mainasara, wanda ya mulki kasar daga 1996 kafin a kifar da gwamantinsa a juyin mulkin da aka kashe shi a 1999.
- 2023: Magoya bayan Tinubu na taron rantsar da shugabannin jihohi
- Kwamitin Wa’azi: An ja daga tsakanin gwamnati da malamai
Alkalan kotun mai zama a birnin Abidjan na kasar Kwaddabuwa sun yanke hukuncin biyan kudaden ne a matsayin diyyar abin da magadan marigayin suka kashe na kudaden shari’a.
Sanarwar da kakakin kotun, Elohor Ovadje, ya fitar ta ce kudaden, kamar da lauyan iyalan Bare Mainasara, Chaibou Abdourahaman, ya bayyana sun hada da kudaden daukar lauyoyi da na tafiye-tafiye da na harajin VAT da sauransu.
Mai Shari’a Dupe Atoki, wanda ya karanta hukuncin kotun, ya ce alkalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan karar da iyayalan Janar Bare Mainasara suka kara shigarwa a shekarar 2020, suna neman kotun ta fayyace yawan kudaden da gwamnatin kasar za ta biya su.
Iyalan mamacin sun bukaci hakan ne saboda hukuncin da kotun ta yanke a shekarar 2015 bai ambaci yawan kudaden ba, duk da cewa kotun ta ce, “Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ce za ta biya dukkannin kudaden da suka danganci shari’ar.”
– Abin da ya faru a kotu –
Lauyan masu kara, ya shaida wa kotun cewa suna neman a gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta biya su 83,732,317 CFA, wanda suke so kotun ta ba da umarnin a gaggautan biyan su.
Sun bukaci hakan ne bisa dogaro da sashe na 69 da ya ce za a biya “Muhimman kudaden da bangarorin suka kashe a shari’ar, musamman kudaden tafiye-tafiye da na sallamar lauyoyi da mashawarta da ejen-ejen.”
A martaninta, lauyar gwamnatin, Aissatou Zada, ta nemi kotun ta yi watsi da bukatar iyalan tsohon shugaban Bare Mainasara, bisa hujjar cewa Sashe na 70.
Sashen ya ce “Duk lokacin da aka samu sabani kan kudaden da za a biya, idan aka kai wa kotun korafi za ta sauri bangaren da ake kara, sannan ta bayar da umarni ko ta fitar da sanarwa a kan hakan bayan ta yanke hukunci.”
Hakan, a cewarta, na nufin sai masu karar sun gabatar da shaidar abin da suka kashe, sannan bangaren gwamnati ya mayar da martani; Sannan tunda har kotun ta yanke hukunci da farko cewa gwamnati ya biya kudin, to maganar ta kare.
Har ila yau, iyalan ba su da hurumin zama wadanda za su tantance abin da suka kashe, su gabatar wa kotun, saboda haka ya kamata kotun ta yi watsi da bukatar.
Sai dai kotun ta ce a karkashin Sashe na 70, iyalan Bare Mainasara na da ’yancin lissafa kudaden da suka kashe su gabatar mata, ita kuma ta yi alkalanci kan iya abin da za a biya su, bayan ta yi nata tantancewar.
Saboda haka ta ba da umarnin a biya su 7,564,250 CFA a matsayin kudaden lauyoyi da na tafiye-tafiye, amma ta yi watsi da sauran kudaden da iyalan suke nema a biya su.
Sauran alkalan da suka yanke hukuncin su ne Mai Shari’a Gberi-Be Ouattara da Mai Shari’a Januaria Costa.
A zaman kotun na ECOWAS da zai ci gaba na tsawon mako biyu ana sa ran alkalan za su saurari kararraki 38, sannan su yanke hukunci a kan shari’o’i 11.