✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Duniya ta daure Bemba shekara 18

Kotun Hukunta Masu Aikata Miyagun Laifuffuka ta Duniya (ICC), ta yanke wa tsohon Mataimakin Shugaban kasar Kongo Mista Jean Pierre Bemba hukuncin daurin shekara 18…

Kotun Hukunta Masu Aikata Miyagun Laifuffuka ta Duniya (ICC), ta yanke wa tsohon Mataimakin Shugaban kasar Kongo Mista Jean Pierre Bemba hukuncin daurin shekara 18 a gidan yari.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito cewa a ranar Talata ce Kotun ICC ta yanke wa Bemba wannan hukunci bisa samunsa da aikata laifuffukan yaki da cin zarafin mutane.
Mista Bemba zai yi shekara goma ne a gidan yarin, ganin cewa ya riga ya shekara takwas a tsare.
Kotun dai ta samu dakarun da Bemba yake mara wa baya mai suna Congolese Liberation Army da laifin kai wa fafaren hula hare-hare, a makwabciyar kasar wato Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.
An ce Mista Bemba ya tura dakarun nasa su 1,000 ne domin su je su kara da wata kungiyar ’yan tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. An kuma gano cewa dakarun sun yi amfani da karfin tuwo wajen yi wa mata fyade, baya ga hare-haren da suka rika aiwatarwa a kan fararen hula.
Mai gabatar da kara na Kotun Duniya dai ya so a yanke wa Bemba hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon shekara 25 ne.
Mista Jean Bemba yana samun goyon baya daga jam’iyyarsa ta MLC, kuma ta sha alwashin za ta daukaka kara kan wannan hukunci.