Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta kori Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe bayan soke nasararsa a zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da ya gabata.
A ranar Talata ne kwamitin alkalai uku, ya bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Sa’ad Abdullahi Ibrahim (Turakin-Opanda), a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Umaisha/Ugya ta jihar.
- An gargaɗi ’yan acaɓa kan ɗaukar fasinjoji 2 da daddare a Gombe
- An gano gawar shugaban Fulani a rijiya a Filato
Kazalika kotun, ta tabbatar da nasarar Jacob Ajegana Kudu na jam’iyyar APC, mai wakiltar mazabar Nasarawa Eggon ta Gabas a zaben Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, kotun ta yi watsi da karar da Ibrahim Muhammed dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar, wanda ke kalubalantar sakamakon zaben da aka yi.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, Kudu ya sadaukar da nasararsa ga ikon Allah, inda ya nuna godiya ga bangaren shari’a bisa yadda suka bi ra’ayin jama’a tare da jaddada aniyarsa ta yi wa ‘yan mazabar hidima.