✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara ta kori Abba Gida-Gida a matsayin Gwamnan Kano

Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba shi da lasisi a hukumance na zama dan jam’iyyar NNPP.

Kotun Daukaka Kara da ke yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Kano, ta ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP bai cancanci tsayawa takara ba a Zaben Gwamnan Kano da aka gudanar a watan Maris.

A yau Juma’a ce Kotun Daukaka Kara take yanke hukunci kan tankiyar da ta dabaibaye zaben gwamnan Kano.

An dai gudanar da zaben ne tun a wata Maris, inda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai daga bisani jam’iyyar APC ta garzaya Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, tana mai neman a sake nazari kan lamarin, inda ta samu nasara kotun ta ce dan takararta, Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben.

Kan haka ne NNPP ta garzaya Kotun Daukaka Kara tana mai neman hakki, inda bayan sauraron korafi da hujjojin kowane bangaren a makon jiya, ta ce za ta sanar da hukuncin a wannan Juma’ar.

Sai dai a zaman na wannan Juma’ar da ya gudana a Abuja, Kotun ta jaddada hukuncin Alkalan Kotun Sauraron Kararrakin da suka tabbatar cewa babu sunan Abba a rajistar ’ya’yan da Jam’iyyar NNPP ta bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), don haka bai cancanci tsayawa takara a karkashin inuwar jam’iyyar ba.

Manyan hujjoji NNPP da kotun ta yi fatali da su

Ana iya tuna cewa Kotun Sauraron Kararrakin Zaben dai ta yanke hukuncin ne ta manhajar zoom, lamarin da lauyoyin NNPP suka ce suna adawa da shi.

A cewar Kotun Daukaka Karar, “gabatar da hukunci ta manhajar zoom ba laifi bane.

Sannan duk da Gawuna baya cikin masu kara, zai iya amfana da hukuncin kotu idan aka tabbatar da cancantarsa.

Saboda haka ba dole ba ne sai APC ta saka sunan Nasir Gawuna wajen shigar da kara.

Haka kuma, kotun ta kafa hujjar cewa sashe na 177 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wajibi sai ne mutum ya zama dan jam’iyya kafin ya cancanci tsayawa takara.

Gawuna ne ya ci Zaben Kano — Kotun Sauraron Kararrakin Zabe

Ana iya tuna cewa, a watan Satumbar da ya gabata ne Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.

Kotun ta soke ƙuri’u 165,663 kuma ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta janye shaidar nasarar da ta miƙa wa Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, sun soke kuri’un ne bisa hujjar cewa ba su da hatimin INEC a jikinsu, wanda hakan ya saba wa Dokar Zabe, don haka ba halastattun kuri’u ba ne.

Hakazalika a zaman kotun ta amince da dukkan bukatun da APC ta yi mata na cewa Abba ba halastaccen dan jam’iyyar NNPP ba ne, wanda hakan ya saba wa Dokar Zabe ta 2022 sannan an yi amfani da kuri’un bogi a zaben.

Bayan Zaben Gwamnan Kano da aka gudanar a watan Maris, INEC ta sanar cewa Abba ne ya lashe zaben da ratar kuri’u 128,900, inda ya samu jimillar kuri’u 1,019,602, inda Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.

An tsaurara tsaro a Kano

Rundunar ’yan sandan a Kano ƙarƙashin kwamishinanta, Mohammed Usaini Gumel, ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin jam’iyyun APC da NNPP a jajiberen ranar yanke hukunci.

Ta ce sun ɗauki matakai da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin ba a fuskanci rashin zaman lafiya a yayin, da kuma har bayan hukuncin kotun ba.

Kwamishina Mohammed Usaini ya kuma ce, sun tattauna, kuma sun samu tabbaci daga shugabannin jam’iyyun biyu cewa za su yi duk abin da ya wajaba don ganin ba a kawo hargitsi, saboda hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba a Kano.

Me ya rage?

Akwai damar sake ɗaukaka ƙara ta ƙarshe ga duk ɓangaren da bai gamsu ba, zuwa gaban Kotun Ƙolin Najeriya, wadda ita ce kankat.