Majalisar Dattawa ta amince da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.
Amincewar majalisar ta bukatar hakan da Shugaba Buhari ya aike mata ya biyo bayan rahoton Kwamitin Shari’a da Hakkin Dan Adam na Majalisar.
Shugaban Kwamitin Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem wadda alkali ce a Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta cancanci nadin.
- Buhari ya ayyana Dongban-Mensem Shugabar Kotun Daukaka Kara
- Buhari na neman amincewar Majalisa kan Dongban-Mensem
Sanata Opeyemi ya shaida wa takwarorinsa cewa babu wani korafi da kwamitinsa ya samu a kan wadda ake son nadawan.
Mai Shari’a Dongban-Mensem alkali ce a Kotun Daukaka Kara, wadda Hukumar Kula da Harkokin Sharia ta Kasa (NJC) ta gabatar wa Shugaban Kasa sunanta domin nada ta a mukamin.
A ranar 8 ga watan Yuni, 2020 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ta a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara na riko.
Buhari ya sanar da hakan ne a takardar bukatar amincewa da nadinta a takardar da ya aike wa Majalisar Dattawa.
Hadimin Sugaban Kasa a kan Yada Labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a cikin sanarwar da ya fitar a yammacin nan.
A ranar 9 ga watan Yunin ne shugaba Majalisa Ahmed Lawan ya karanta takardar Buhari a zauren majalisar sannan ya umurci kwamitin Shari’a da ya yi aiki a kan bukatar shugaban kasar ya mika rahoto.