Kotun Ƙolin ta yi watsi da wata ƙara wadda take ƙalubalantar dokar da ta kafa Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa.
Tun farko dai Atoni-Janar na jihohi 16 ne suka shigar da ƙarar inda suke buƙatar rushe hukumar da wasu takwarorinta biyu.
Sauran hukumomin da masu shigar da ƙara ke neman a rushe sun haɗa da Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ICPC da kuma Hukumar Lura da Harkokin Kuɗi ta NFIU.
- HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja
- Za mu ranto Naira tiriliyan 9 domin cike giɓin Kasafin Kuɗin 2025 — Gwamnatin Tarayya
Sai dai Alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani-Abba-Aji da suka yanke hukuncin, baki ɗayansu sun yi watsi da ƙarar da aka shigar sakamakon rashin cancanta.
Jihohin da suka fara shigar da ƙarar sun haɗa da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nassarawa, Kebbi, Katsina, Sakkwato, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Filato, Kuros Riba da Neja.
Sai dai kuma da a yayin da aka ci gaba da sauraren ƙarar a ranar 22 ga Oktoba, jihohin Imo da Bauchi da kuma Osun sun shiga shari’ar a matsayin masu taya shigar da ƙara, sai dai kuma Anambra da Ebonyi da Adamawa sun sanar da janyewa daga ƙarar.
Ana iya tuna cewa an kafa Hukumar EFCC ne ta hanyar dokar Majalisar Dokokin Tarayya a ranar 12 ga watan Disambar 2002, a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Bayan kafa hukumar ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya zama shugabanta na farko inda hukumar ta soma aiki a ranar 13 ga Afrilun 2003.