Jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kan hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke kan zaben gwamnan jihar.
Shugabannin jam’iyyun sun kulla yarjejeniyar ne a hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar Kano a gaban kwamitin shugabannin hukumomin tsaro.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Usaini Muhammad Gumel, ya ce shugabannin jam’iyyun sun sabunta alkawarinsu na tabbatar da zaman lafiya a lokacin da kotu ta sanar da hukuncin da ta yanke da kuma a yayin bikin murnar nasara.
Ya ce taron ya tattauna kan wasu miyagun ’yan siyasa da ke yunkurin haɗawa tashin hankali a jihar, sannan ya yaba wa shugabannin APC da NNPP kan yadd tsayuwarsu a karo na bisa alkawarin da suka dauka da farko na zaman lafiya.
- Kotu ta rufe aususun Gwamnatin Kano a CBN da sauran bankuna —Lauyan ’yan kasuwa
- Tarihi da rayuwar ’yan Afirka da ke kula Kabarin Manzon Allah (SAW)
Usaini Gumel ya ce taron ya kuma tattauna kan matsalar shugabanci a cikin jam’iyyun biyu a wasu kananan hukumomin jihar.