Wata Kotun Sfaniya ta yanke wa tsohon ɗan wasan Barcelona da Brazil Dani Alves hukuncin cin sarƙa ta shekara huɗu da watanni shida.
Kotun ta yanke wa Alves hukuncin ne bayan samunsa da a laifin yi wa wata mata fyaɗe a wani gidan rawa a birnin Barcelona.
- Sanwo-Olu ya bullo da hanyoyi 3 na kawo wa mazaunan Legas sauƙin rayuwa
- Jama’a sun daka wa motocin abinci wawa a hanyar Abuja
Tun a watan Janairun 2023 ne Alves mai shekara 40 ya shiga hannu, inda ya musanta zargin cin zarafin da ake yi masa na cin zarafin matar tun a ƙarshen watan Disambar 2022.
Bayan hukuncin na wannan Alhamis ɗin , lauyarsa ta nuna rashin gamsuwa tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Lauyan wadda take ƙara ya yi maraba da wannan hukunci, yana cewa hakan yana tabbatar da abin da suke yaƙi akai a tsayar da gaskiya, kan wadanda aka zalunta.
Yayin da za a miƙa ɗan wasan gidan yari na shekara hudu da rabi, kotun ta ce za a ƙara yi masa ɗaurin shekara biyar da za a riƙa bibiyar abin da yake yi.
Mai gabatar da ƙarar ya nemi a ɗaure shi na shekara tara.
A Sfaniya dai, ana binciken duk wani iƙirarin fyaɗe ƙarƙashin zargin cin zarafin lalata, kuma idan aka samu mutum da laifin akan yanke masa shekara 15 a gidan yari.
Matarsa Joana Sanz mai shekara 31, ta ce ya ranar da abin ya faru ya koma gida ne a buge, lamarin da kotun ta ce buguwarsa ba za ta sauya masa halayyarsa ba.
Tun da fari ya musanta sanin matar da ta yi zarginsa amma dai daga baya ya ce ya santa sun haɗu a banɗaki amma dai babu abin da ya faru tsakaninsu.
Amma daga baya ya ƙara bayanin cewa sun yi wasu ’yan abubuwa da suka jiyar da junansu dai.
Alves ya buga wa Barcelona sama da wasanni 400, ya ci La Liga shida ya ci Kofin Zakarun Turai uku. Kuma yana cikin tawagar Brazil da ta je gasar Kofin Duniya ta 2022.
Ya lashe kofina da yawa a lokacin da ya zauna a Sevilla da Juventus da kuma PSG, kuma shi ne ya fi buga wasa a Brazil, inda ya buga wasa 126.
Alƙaluma sun tabbatar da cewa Alves na ɗaya daga cikin ’yan wasan kwallon da suka fi samun kyautuka a tarihi.