✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da karar da Ebans ya shigar ta neman diyyar Naira miliyan 300

Wata Kotun Tarayya a karkashin mai shari’a Abdul’aziz Anka a Legas, ta kori karar da hamshakin attajirin nan kuma wanda ake tuhuma da garkuwa da…

Wata Kotun Tarayya a karkashin mai shari’a Abdul’aziz Anka a Legas, ta kori karar da hamshakin attajirin nan kuma wanda ake tuhuma da garkuwa da mutane da amsar kudin fansa, Chukwudumeme Onwuamadike (Ebans) ya shigar a kwanakin baya, inda ya nemi a biya shi Naira miliyan 300 saboda tsare shi da ’yan sanda suka yi a wajensu, kafin a kai shi kotu. Ya shigar da karar ce da nufin an keta masa ’yancinsa na dan Adam.

A karar, ya nemi kotu da ta umurci ’yan sanda su kai shi kotu nan take ko kuma su sallame shi ta hanyar beli. Haka kuma ya yi korafin cewa a jefa shi cikin yamadidi a kafafen watsa labarai, a lokacin da aka kama shi. Sai dai kotun ba ta biya masa wadannan bukatu ba, ta kori karar saboda rashin cancantarta, kamar yadda mai shari’ar ya bayyana.

Shi dai Ebans, ya shigar da karar bukatarsa ta a biya shi Naira miliyan 300 ne ta hannun lauyansa, Olukayode Ogungbaje, inda ya zargi Sufeto Janar na ’yan sanda da take masa ’yancinsa, wajen tsare shi ba tare da bin hanyoyin da shari’a ta amince ba. A cikin karar, ya hada har da Hukumar ’yan sanda ta kasa da Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Legas da Sashin Yaki da fashi da mamaki a Jihar Legas (SARS).

Lauyan ya ce wa kotu, tsarewa da rufe Ebans da aka yi daga ranar 10 zuwa 22 ga Yunin 2017 ba tare da an kai shi kotu ba, wanda  a cewarsa, wannan keta hakkinsa ne na dan Adam kuma ya saba wa Sashi na 36 na Kundin Tsarin Mulki ne.

Sai dai a ta bangaren ’yan sanda, lauyansu ya bayyana cewa wannan kara ba ta bisa hanya, don haka ya roki kotu da ta kore ta, domin a wajen gudanar da aikinsu na kamawa da tsare Ebans, ba su aikata wani laifi ba.

A yayin da yake yanke hukunci, mai shari’a Anka ya hukunta cewa, tsare mai laifin da aka yi daga ranar 10 zuwa 22 na Yunin bara, daidai ne, yana kan hanya a hukumance. Domin kuwa ’yan sandan sun shaida wa kotu batun tsarewar kuma sun samu umurnin tsare shin a tsawon kwanaki 90.

Game da batun cewa an yayata al’amarinsa a kafafen watsa labarai kuwa, mai shari’ar ya bayyana cewa babu wata doka da ta haramta wa ’yan jarida gudanar da aiukinsu, don haka sai ya bayyana cewa: “Na sallami wannan kara bisa wadannan dalilai.”