✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yi watsi da daukaka karar wanda ake zargi da wakar batanci a Kano

Kotun ta ce hukuncin kotun farko yana kan ka’ida

Kotun Daukaka Kara da Kano ta yi fatali da karar da mawakin nan da ake zargi da yin wakar batanci, Aminu Yahaya Sheriff ya daukaka kan hukuncin kisan da aka yanke masa.

Mawakin dai ya daukaka karar ce yana neman a sake yi masa shari’ar da ka kai ga yanke masa hukuncin tun da farko.

Sai dai Kotun Daukaka Karar ta ce Kundin Shari’ar Musulunci na jihar Kano na shekara ta 2000 bai saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba.

Da yake yanke hukuncin ta bidiyo ranar Laraba, alkalin kotun, Mai Shari’a Abubakar Mu’azu Lamido, ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba jihohi damar yin dokokinsu ta hannun Majalisun Dokokinsu.

Aminu Sheriff, wanda a watan Agustan 2020 ne wata kotun Shari’ar Musulunci ta yanke masa hukuncin kisa dai ya nemi Babban Kotun jihar Kano ta yi watsi da hukuncin.

A watan Nuwamban shekarar ta 2020 dai kotun ta soke hukuncin, inda ta yi umarnin sake yi masa shari’ar, saboda cewa ba a bi ka’idojin da suka kamata ba a cikin shari’ar ta farko.

Kundin Shari’ar Musulunci na Jihar Kano ma shekarar 2000 dai ya tanadi hukuncin kisa kan duk wanda aka tabbatar ya aikata batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), wanda a kansa ne ake tuhumarsa.