Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta yi fatali da da’awar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, kan cewa Shugaba Bola Tinubu ba dan Najeriya ba ne.
Atiku ya kuma zargi Tinubu da cewa ya taba yib harkallar miyagun kwayoyi a kasashen waje a shekarun baya.
- Kotu ta kori karar LP kan samun kaso 25 a Abuja kafin a lashe zabe
- Jam’iyyar LP ta yi watsi da hukuncin kotu kan zaben Shugaban Kasa
Da take yanke hukunci a kan bukatar neman soke cancantar Atiku, kotun karkashin Mai Shari’a Moses Ugo, ya ce da’awar Atiku ba ta da tushe ballantana makama.
Atiku ya kuma roki a hana Tinubu takarar Shugaban Kasa saboda an taba kwace masa Dalar Amurka 460,000 domin a wanke shi daga zargin badakalar kwayoyi a wata kotun Arewacin birnin Illinois na Amurka.
Ya kuma yi zargin cewa Tinubu bai bayyana a jikin fom din da ya cike ya mayar wa INEC cewa yana da takardar shaidar zama ɗan Najeriya da ta kasar Guinea ba.