✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi wa wani mutum allurar mutuwa a Amurka

Alkalai 11 ne cikin 12 suka ba da shawarar zartar da hukuncin kisan.

Jihar Alabama ta Amurka ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ya kashe wata mata da duka a shekarar 2001.

Wannan lamarin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito na nuna alamar dawo da zartar wa da mutane hukuncin kisa ta hanyar allurar mutuwa bayan dakatar da hakan da aka yi a baya.

An sanar da cewa James Barber mai shekara 64 ya cika ne da misalin karfe 1:56 na safiya, bayan da aka yi masa allurar guba a gidan yarin da ke Kudancin Alabama a ranar Juma’a.

An yanke wa Barber hukuncin kiasa ne sakamakon kashe wata mata mai shekara 75 mai suna Dorothy Epps.

Masu shigar da kara sun ce Barber ya amsa laifinsa na kai wa Epps hari da guduma sannan ya tsere da jakarta.

Alkalai 11 ne cikin 12 suka ba da shawarar zartar da hukuncin kisan.

Shi ne kisa na farko da aka zartar a Alabama a bana bayan da jihar ta dakatar da yin hakan a bara.

Gwamnan Alabama Kay Ivey ya sanar da dakatar da zartar da hukuncin kisan a watan Nuwamban bara bayan sake duba hanyoyin da ake bi wajen yin hakan.

Matakin na zuwa ne bayan da jihar ta dakatar da yin wasu allurai biyu na guba saboda matsalolin da aka samu wajen tura su a jijiyoyin maza da ke lalata su.

Kungiyoyin wayar da kai sun yi ikirarin cewa hukuncin kisa na ukun ma ya gamu da tarnaki, lamarin da jihar ta musanta.

Lauyoyin Barber ba su samu nasarar da kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin ba, inda ya kafa hujja da cewa “ana samun matsala wajen yin allurar gubar.”

Gwamnatin jihar ta bai wa kotuna umarnin aiwatar da hukuncin kisan.

“Mrs. Epps da iyalanta sun shafe shekara 22 suna jiran a yi musu adalci,” kamar yadda ofishin atoni janar na Alabama ya rubuta wa kotun.

An zartar wa Barber hukuncin kisa ne sa’o’i kadan bayan da a Jihar Oklahoma ma aka zartar wa da Jemaine Cannon hukuncin kisa kan laifin daba wa wata mata mai suna Tulsa wuka a shekarar 1995 bayan da ya tsere daga gidan yari.