✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa tsohon dan sanda hukuncin daurin rai-da-rai saboda kisan kai

Wata Babbar Kotu a Legas karkashin jagorancin Mai Shari’a Adenike Coker, ta yanke wa wani tsohon dan sanda, Olalekan Ogunyemi, hukuncin daurin rai da rai…

Wata Babbar Kotu a Legas karkashin jagorancin Mai Shari’a Adenike Coker, ta yanke wa wani tsohon dan sanda, Olalekan Ogunyemi, hukuncin daurin rai da rai a kurkuku bayan kama shi da laifin kashe wani mai suna Kolade Johnson.

Bayanai sun ce Ogunyemi ya harbi marigayin da bindiga a ranar 31 ga Maris, 2019 a wani gidan kallon kwalo da ke yankin Ikeja.

Johnson na kallon wasan da ake bugawa tsakanin Liverpool da Tottenham Hotspur inda bisa karar kwana ajalinsa ya cim masa.

Da yake yanke hukuncin, Alkali Coker ya samu mai kare kansa da aikata laifin da ake tuhumarsa tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Lauya Jubril Kareem ne wanda ya wakilci Jihar Legas, yayin da lauya Abayomi Omotubora ya tsaya wa wanda ke kare kansa a yayin zaman shari’ar da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Dokta Oluwaseun Williams ya ba da shaida a gaban kotun, inda ya ce marigayin ya ji raunuka daban-daban har guda shida sakamakon harbin bindiga.