✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin rataya a Kano

Kotun ta same su ne da laifin kisan kai

Babban Kotun Jihar Kano mai lamba biyu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kisan kai.

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a yusuf Ubale, ta sami Samaila Salisu da kuma Aminu Salisu da laifin kashe wani mai suna Ibrahim Alhassan.

Mutanen dai mazauna kauyen Magangara ne da ke Karamar Hukumar Kura ta Jihar.

Sun shiga gidan marigayin ne da nufin aikata fashi da makami, inda a kokarinsu na yin haka, suka harbe shi.

An dai tuhume su ne da aikata hadin baki, kisan kai da kuma tayar da zaune tsaye, laifukan da kotun ta ce sun saba da sassa na 97, 221 (B) da na 114 na kundin Penal Code. Sai dai sun musanta aikata laifukan.

Lauyan masu shigar da kara, Barista Bashir Saleh, ya gabatar da shaidu har guda tara, ciki har da wasu ganau su uku, da kuma wasu hujjoji guda tara, ciki har da wata bindiga da kuma adda.

Bayan sauraron shaidu da hujjojin da aka gabatar, alkalin ya ce kotun ta gamsu da su.

Daga nan ne ya yanke wa mutum biyun hukuncin kisa ta hanyar rataya, sannan ya kara musu da daurin wata shida ko biyan tarar Naira 200,000.

Kazalika, bisa samun su da laifin tayar da hankalin jama’a, kotun ta kara musu da karin hukuncin daurin shekara daya ko biyan tarar Naira 20,000.