Kotu a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin bulala tare da biyan tarar Naira 10,000 kowannensu.
Kotun Majistaren ta yanke hukuncin ne bayan ta kama matashin mai shekaru 25 da laifin sayar da miyagun kwayoyi, addabar al’umma da kuma mallakar sholisho da sukudaye masu gusar da hankali.
- Ina tallan doya don tsare mutuncina —Gurgu
- An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina
- Boko Haram ta hallaka mutum 13 a arewacin Kamaru
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
Bayan Mai Shari’a Farouk Ibrahim ya karanto masa laifin da ake tuhumarsa, sai ya matashin amsa da cewa ya aikata.
Da yake yi wa kotun jawabi, Mai gabatar da kara, Lamido Soron-Dinki, ya ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin wani samame da suka kai a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.