✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa magidanci daurin rai-da-rai bisa yi wa tsohuwa fyade

Ya yi wa tsohuwar mai kimanin shekara 85 fyade

Wata Babbar Kotun Jihar Ekiti mai zamanta a Ado-Ekiti, ta yi wa Durodola Ogundele mai shekara 65 daurin rai-da-rai bayan da ta kama shi da laifin yi wa wata tsohuwa mai shekara 85 fyade.

A cewar karar, an sami Ogundele da laifin yi wa tsohuwar fyade ne a ranar 15 ga watan Yunin 2021, a yankin Ayetoro Ekiti da ke cikin Karamar Hukumar Ido/Osi a Jihar.

Laifin da alkalin kotun, Mai Shari’a Monisola Abodunde, ta ce ya saba wa sashe na biyu na dokar harmcin saba wa jinsi na Jihar Ekiti na 2019.

Da take ba da shaida a gaban kotun, yarinyar tsohuwar da lamarin ya shafa, Opeyemi Bolaji ta ce, “A lokacin da na zo don bai wa mahaifiyata abincin karin safe, da na isa, sai na tarar da ita cikin halin da ba daidai ba.

“Da na matsa mata da neman sanin abin da ya faru, sai ta ce mini wanda ke kare kansa bai bari ta yi barci ba, ta ce ya shiga dakinta da misalin karfe 1:00 na dare sannan ya shafa mata mai a ilahirin jikinta, har da gabanta da kuma bayanta, ya yi mata tausar jiki, ya ts0tsi mamanta sannan ya kwanta da ita da karfin tsiya.

“Amma da na yi kokarin bincike daga bangaren mai kare kansa, sai ya ce mini da alama dai mafarki ne mahaifiyar tawa take yi,” inji yarinyar.

Da farko, an soma kai karar batun ga ofishin ‘yan sanda da ke Ido Ekiti kafin daga bisani aka tura batun zuwa Sahen Binciken Manyan Laifuka na babban ofishin Rundunar ‘Yan Sandan da ke Ado Ekiti.

Mai tuhuma, Folasade Alli, ta gabatar wa kotun shaidu guda biyar don tabbatar da wanda ake zargin mai laifi ne.

Haka nan, sakamakon bincikenta da kuma bayanan da likita ya hada kan batun baya binciken da ya yi, duk ta tattara ta gabatar wa kotun.

Mai kare kansa ya yi bayani a gaban kotun ne ta bakin lauyansa M.O. Folorunso, wanda ko shaida guda ya kasa gabatarwa don kare kansa.

Da take yanke hukuncin, Alkali Monisola Abodunde ta ce, lallai mai kare kansa ya aikata lafin da ake tuhumarsa da aikatawa.

“Don haka ba tare da wani kokwanto ba, mai tuhuma ta gabatar da gamsassun hujjojin da suka tabbatar cewar da hankalinsa wanda ake zargin ya kwanta da tsohuwar kuma ta karfi bayan ya shafe mata jiki da al’aurarta da mai”.

Daga nan, kotun ta kama Ogundele da laifin fyade tare da yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a gidan yari daidai da laifin da ya aikata.

(NAN)